Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Wani masanin harkokin shari’a kuma Malami a tsangayar koyar da harkokin Shari’a a Jami’ar Bayero dake Kano Dr. Nuhu Musa Idris ya kalubalanci matakin da jami’an tsaro suke dauka na yin bidiyo ga wadanda ake zargi da aikata laifi, wanda ya ce hakan ba daidai ba ne.
Kadaura24 ta rawaito Dr. Nuhu Musa Idris ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da wata makala a wata bitar yini guda da kungiyar Citizen for Development and Education CDE ta shiryawa yan jarida a Kano.
“A matsayina na wanda ya shafe sama da Shekaru 20 Ina aikin lauya kuma Ina koyar da dalibai harkokin Shari’a, har yanzu banga wata doka da ta baiwa jami’an tsaro damar yiwa mai laifi bidiyo kuma har a yada a kafafen sada zumunta ba”. A cewar Dr. Nuhu Musa

Dr. Nuhu Musa Idris ya ce Idan akwai waccan dokar don Allah yana so a fada masa ita ko a nuna masa ita domin ya karu, tun da shi mai neman Ilimi ne.
“A doka duk wanda ba alƙali ba ne ya yanke masa hukunci ba dace a kirawo shi da mai laifi ba, daga lokacin da jami’an tsaro suka kama shi ko aka kawo shi sunansa wanda ake zargi, idan kuma aka gabatar da shi a Kotu sunansa wanda ake tuhuma, ba zai zama mai laifi ba har sai lokacin da alkali ya tabbatar da cewa an kama shi da laifin da ake tuhumasa”. Inji Dr. Nuhu Musa Idris
Kannywood Ta Yi Rashin Babban Mawaki
Ya ce ta iya yiwuwa wanda aka yiwa bidiyo aka yada shi a kafafen sada zumunta kuma idan an je Kotu, Kotu ta ce ba ta same shi da laifin ba, kuma an rika an bata masa suna.
Ya bukaci jami’an tsaro da su tabbatar suna gudanar da aiyukansu akan dokokin da suka kafa su da kuma dokokin kasa.