Daga Abubakar Yakubu
Shugaban kungiyar nan mai zaman kanta ta Citizen for Development and Education ( CDE) Amb. Ibrahim Waiya ya bukaci yan jarida da su kasance masu yawaita bincike da neman ilimin domin kyautata Aikinsu da samun damammaki.
” Akwai damammaki da yawa da ake samu a kasashen duniya, kuma ba zaka same su ba sai ka fadada kunaninka ka zamo mai kirkira ta fannin aikinka, hakan shi zai sa kafafen yada labarai na kasashen wajen su nemeka kar ka cimma burkina na rayuwa”.
Amb. Ibrahim Waiya ya bayyana hakan ne yayin wata bitar yini guda da kungiyar ta CDE ta shiryawa yan jarida a kano kan yadda za su inganta aiyukansu.


Ya ce aikin jarida a wannan lokacin yana samun sauye-sauye musamman saboda zuwan sabbin fasahohi , don haka akwai bukatar yan jarida a rika karbar sauye-sauyen domin aiyukansa su rika tafiya dai-dai da zamani.
” Mun shirya muku wannan bitar ne domin sake tunatar da ku muhimmancin bin ka’idoji da dokokin aikinku , don al’umma su amfane ku yadda ya kamata saboda kuna da matukar muhimmaci a cikin al’umma shi yasa muke so ku inganta aiyukan naku”. Inji Amb. Waiya
Amb. Ibrahim Waiya ya sha alwashin cigaba da hada kai da yan jarida domin samar da cigaba mai ma’ana ga al’ummar jihar Kano da kasa baki daya.
Dr. Bala Muhammad na Jami’ar Bayero dake Kano ya gabatar da makala mai taken “Bin ka’idoji da dokokin aikin jarida ga Manema labarai, yayin da shi kuma Dr. Nuhu Musa Idris shi ma daga jami’ar Bayero ya gabatar da makala mai taken ” Rabe-raben Gwamnatin Nigeria da dokokinsu”.