Daga Rahama Umar Kwaru
Allah ya yiwa shahararren mawakin nan na masana’antar shirya fina-fina ta kannywood Muhammad Mu’azu Birniwa wanda aka fi sani da El-Mu’az Birniwa rasuwa.
El-Muaz Birniwa ya yanke jiki ya fadi ne a dai-dai lokacin da suke tsaka da buga Kwallon kafa ta Angoncin mawaki Auta Waziri a garin Kaduna jiya laraba.
Rahotanni na jaridar KADAURA24 ta samu sun nuna cewa yana cikin fili ana buga wasa haki ya kama shi inda ya yanke jiki ya fadi bayan an kai shi asibiti ne likitoci suka tabbatar da cewa ya rasu.

Za dai a yi jana’izarsa yau alhamis a masallacin Zangon Daura dake NDC unguwar kaji a jihar Kaduna da misalin karfe 1 na rana.
El-Mu’az Birniwa dai kafin rasuwar sa ya bada gudunnawa sosai wajen cigaban masana’antar kannywood musamman a inda ya yi shura wato wakoki.
Allah yajikansa da Rahama Allah ya bawa yan uwansa da masoyansa hakurin rashinsa ameen