Daga Rahama Umar Kwaru
Wata Kungiya dake tallafawa a jihar kano mai suna Kano Network for Orphans and human development ta samu nasarar horas da marayu 300 sana’o’in hannu da koyar da su haddar Al-Qur’ani a wani bangare na ganin ta inganta rayuwar marayu a jihar.
An horar da marayun ne waɗannan sana’o’i da haddar al’qur’anin da nufin kyautata halayensu da dabi’unsu don samu zamo masu mutane na gari da al’umma za su yi alfahari da su.
A jawabinsa na maraba shugaban kungiyar Kwamared Adam Umar ya bayyana cewa tallafawa marayu yana da matukar mahimmancin gaske a nan duniya da Kuma gobe kiyama.

Ya ce, “Suna bukatar sanin Allah Sannan su sami ilimin sana’o’in da zasu iya dogara da kawunansu ta yadda zasu gudanar da kyakykyawar rayuwa”.
Dagacin da ya Shekara 91 yana mulki ya Rasu
Da yake jawabi a madadin kwamishinan ilimi na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, wanda ya wakilce shi Hon. Habeeb Hassan El-Yakub, mataimaki na musamman ga gwamna kan koyar da sana’o’i ya yaba da kokarin kungiyar na tallafawa shirye-shiryen gwamnati na koyawa matasa sana’o’in hannu.
Ya kuma yi alkawarin cewa nan ba da dadewa ba gwamnatin jihar za ta samar da cibiyoyin koyar da sana’o’in hannu a dukkanin kananan hukumomin jihar Kano 44, sannan ya yi alkawarin tallafa wa kungiyar domin ta gina matsuguninta na din-din-din.
Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Dr. Muhammad Isa Umaru wanda Wazirin Rano ya wakilta, Mal. Kabiru Sani, ya yabawa kungiyar Marayu da cigaban bil Adama ta Kano bisa jajircewarta na tallafawa marayun.
A yayin taron an kuma karrama mutanen da suka bayar da gudunmawa sosai wajen jin dadin marayu.