Daga Sharifiya Abubakar
Dan majalisar tarayya mai wakilar kananan hukumomin Ghari da Tsanyawa Engr. Sani Bala Tsanyawa ya ce sannu a hankali sai an rasa dan Kwankwasiyya a kananan hukumomin da yake wakilta.
” Sakamakon aiyukan alkhairin da muke yi a Ghari da Tsanyawa yanzu haka Mun karɓi yan Kwankwasiyya masu tarin yawa wadanda suka ce sun Ajiye tafiyar sun dawo jam’iyyar ta APC mai tarin Albarka”. Engr.
Dan majalisar ya bayyana hakan ne a jiya talata lokacin da ya karɓi wasu magoya bayan jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya na karamar hukumar Ghari, wadanda suka dawo APC karkashin Shugabansu Team Leader Dogon Baro.

Engr. Sani Bala Tsanyawa bayan ya yi musu maraba da dawowa APC , ya kuma ba su tabbacin za a cigaba da mu’amala da su ba tare da nuna musu bambanci ba.
Ya kuma ba su tabbacin zai cigaba da aiyukan alkhairin da shi suka gani har suka dawo APC, Sannan zai cigaba ganin al’ummar kananan hukumomin Ghari da Tsanyawa sun cigaba da sharbar romon dimokaradiyya.
Sani Bala Tsanyawa ya kaddamar da Ginin Asibitin Mata da Yara a Yankinsa
A jawabinsa tun da farki Shugaban tawagar yan Kwankwasiyyar da suka koma Jam’iyyar APC Team Leader Dogon Baro ya ce aiyukan alkhairin da suka ga Engr. Sani Bala Tsanyawa yana yi ne suka sa suka Ajiye tafiyar Kwankwasiyya suka koma Jam’iyyar APC.
” Mun ga kana ta gudanar da aiyukan cigaba a kananan hukumomin nan namu, mu kuma dama muna Siyasa ne saboda cigaban al’ummar mu, shi yasa muka ga ya dace mu zo mu hada kai da kai domin ciyar da yankinmu gaba”. Dogon Baro
Gwamna Namadi ya janye dakatarwar da ya yi wa Kwamishinansa bayan kotu ta wanke shi
Dogon Baro ya baiwa Engr. Sani Bala Tsanyawa tabbacin bashi duk wani goyon baya da yake bukata domin ya cigaba da wakiltar kananan hukumomin Ghari da Tsanyawa a zauren majalisar wakilai ta kasa.
Idan za a iya tunawa a ranar lahadin da ta gabata yayin kaddamar da aikin gini asibitin mata da kananan yara, wasu yan Kwankwasiyya masu tarin yawa sun Ajiye tafiyar Kwankwasiyyar sun koma jam’iyyar APC ta hannun Engr. Sani Bala Tsanyawa Dan majalisar tarayya mai wakilar kananan hukumomin Ghari da Tsanyawa.