Sani Bala Tsanyawa ya kaddamar da Ginin Asibitin Mata da Yara a Yankinsa

Date:

Daga Sharifiya Abubakar

 

Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Tsanyawa da Ghari Injiniya Sani Umar Bala Tsanyawa ya bukaci masu rike da madafun iko a kowanne mataki da su baiwa harkar lafiya fifiko ta hanyar ingantawa.

” Mun damu sosai da harkar da ta shafi lafiya, saboda muhimmancin da take da shi, shi yasa a kowanne lokaci ba na kaza a gwiwa wajen bada tallafi duk abun da ya shafi sha’anin kula da lafiyar al’umma”.

Talla

Tsanyawa ya bayyana hakan ne ne lokacin da yake kaddamar da ginin babban asibiti a mazabar ‘yan kamaye dake karamar hukumar Tsanyawa.

Sani Bala yace aikin gina asibitin za’a yi shi ne tare da gidajen ma’aikatansa, wanda zai lashe kudi fiye da miliyan 200.

Fa’idojin Ayaba Guda Bakwai A Jikin Dan Adam

A cewar Dan majalisar yace ayyukan asibitin idan an kammala shi zai dogara akan Kula da lafiyar Mata da kananan yara.

” Kowa yasan yadda Mata da kananan yara Suke Shan Wahala a sha’anin lafiya, shi yasa a wannan karon na lashi takobin magance matsalolin ta hanyar samar da wannan katafaren asibitin”. Inji Sani Bala Tsanyawa

Kadaura24 ta rawaito cewa asibitin an sanya masa sunan tsohon shugaban karamar hukumar ta Tsanyawa Alhaji Tijjani Abubakar ‘yan kamaye wanda jigo ne ga al’ummar yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...