Daga Sharifiya Abubakar
Sanatan Kano ta Kudu a majalisar Dattawan Nigeria, Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila da dan majalisar tarayya mai wakilar karamar hukumar Bichi Abubakar Kabir Abubakar (Abba Bichi) sun bai wa shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano Hashim Sulaiman Dungurawa awanni 24 ya janye kalaman da ya yi a kansu ko su maka shi a gaban kotu.
A wata takadda mai ɗauke da sa hannun lauyan Kawu Sumaila, Sunusi Musa SAN ya buƙaci da shugaban NNPP a jihar Kano Hashimu Sulaiman Dungurawa ya janye kalaman da yayi masa na zargin cin hanci da maguɗin zabe.
Idan za a iya tunawa kusan kwanaki hudu zuwa biyar kenan Sanata Kawu Sumaila da Hashimu Dungurawa suna ta musayar kalamai kan dambarwar da take faruwa a cikin jam’iyyar NNPP da Gwamnatin jihar kano.

A wata hira da Dungurawa ya yi da wata kafar yada labarai a Kano, ya Zargi Sanata Kawu Sumaila da Karbar cin hanci da kuma karkatar da wasu kudaden da Dungurawan yace an baiwa Sanatan domin gudanar da wasu aiyuka a yankina.
Wannan takadda na zuwa yayin da lamurran siyasa a jihar Kano ke ƙara ɗaukar sabon salo tun bayan yawaitar kiraye-kiraye na cewa gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya tsaya da kafarsa.
Gidauniyar Najashi ta Tallafawa Mata Sama da 100 da Jari da kuma Takardun Daukar Aiki
Haka ma daga bangaren Dan majalisar tarayya mai wakilar karamar hukumar Bichi Abubakar Kabir Abubakar ya bukaci shugaban jam’iyyar NNPPn da ya janye kalaman da yayi akan sa ko ya maka shi a gaban kotu.
Mai magana da yawun Dan majalisar Jamilu Halliru Master ne ya tabbatar da hakan ga jaridar kadaura24.
Inganta Ilimi: Jam’iyyar adawa ta YPP ta Yabawa Gwamnan Jihar Kano
“Ni Jamilu Halliru Master, Babban Darattan Yadda Labarai da Hudda da yan’jarida Na Hon. (Dr) Abubakar Kabir Abubakar Bichi na baiwa Shugaban Jamiyyar NNPP na Kano Hashim Dungurawa Awa 24 ya Gaggauta janye kalamansa na Zargin da ya yiwa Mai girma Dan Majalissar Tarayya Hon. (Dr) Abubakar Kabir Abubakar Bichi na Bawa Sanatan Kano ta Kudu Abdurrahaman Kawu Sumaila kudi. $80m a Lokacin Zabe.
Yanzu abun Jira a gani shi ne shin Dungurawa zai zanje kalaman nasa ko kuwa zai cigaba da tsayawa akan bakarsa.