Rikicin NNPP: Dungurawa ya yiwa Sanata Kawu Sumaila Martani

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Shugaban jam’iyyar NNPP dake mulkin jihar kano Alhaji Sulaiman Hashim Dungurawa ya ce yana nan akan bakarsa ta zargin da ya yiwa Sanatan Kano ta Kudu Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar kano Alhaji Sulaiman Hashim Dungurawa ya Zargi Sanata Kawu Sumaila da karbar rashawar Dala Miliyan 80 daga Shugaban kwamitin kasafi na majalisar tarayya kuma dan majalisar tarayya mai wakilar karamar hukumar Bichi Abubakar Kabir Abubakar.

Sai dai Sanata Kawu Sumaila da Abubakar Kabir Abubakar sun bukaci shugaban jam’iyyar da ya janye kalaman da yayi akansu nan da 24 ko kuma gurfanar da shi a gaban kotu.

Talla

A wata hira da yayi da Freedom Radio Hashim Sulaiman Dungurawa ya ce ba zai janye kalamansa ba, saboda duk wanda yake da mukami dole a zarge shi da cin kuɗin al’umma.

Zargin Rashawa: Kawu Sumaila, Abba Bichi na shirin maka shugaban NNPP na Kano a Kotu

” Ai dole a zarge shi, in har baya son a zarge shi to ya ajiye mukamin da yake kai, ya koma Kasuwa, amma matukar zai cigaba da rike mukamin da mutane suka zabe shi to dole mu zarge shi “. Inji Dungurawa

Da aka tambaye shi shin ko suna wani shiri na daukar mataki akan Sanata Kawu Sumaila? Dungurawa ya ce suna nan suna duba yiwuwar daukar matakai akan shi a jam’iyyance.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...