Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano karkashin jagorancin Abba El-mustapha ta gurfanar da mawaki Dauda Kahutu Rarara a gaban Kotu bisa zargin da sakin wata sabuwar waka batare da salewar Hukumar ba.
A wata sanarwa da jami’in yada labarai na na Hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya aikowa kadaura24, ya ce tun kafin wannan lokaci Hukumar tace fina-finai ta aikawa da mawakin sakon korafi dangane da sabuwar wakar daya saki ba tare da ya kawo an tace ba sai dai mawakin bai bata amsa dangane da korafin da ta aika masa ba wanda hakan ne dalilin da ya sa Hukumar ta garzaya gaban kotun domin kowa zaman doka yake a cewa jami’in Hulda da jama’a na Hukumar.
Wakilan Hukumar a kotu ya tabbatar da cewa tuni kotun ta aikawa da mawakin takardar gayya ta sammaci sai dai ba’a ga fuskar mawakin a kotu ba a yau 13 ga watan nuwamba a yayin zamanta.

Tun kafin wannan lokacin bayan sakin sabuwar wakar Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano ta turawa mawakin sakon neman ba’asi ta hanyar sakon karta kwana sai dai har kawo ya wannan lokaci mawakin bai maidawa da Hukumar amsar sakon ba.
Rikicin NNPP: Dungurawa ya yiwa Sanata Kawu Sumaila Martani
Duk da cewa jami’in hulda da jama’a na hukumar tace Fina-Finan bai bayyana kowacce waƙa ba ce, amma binciken da Jaridar Kadaura24 ta gudanar ya gano cewa an gurfanar da mawakin ne saboda sakin waƙar ” Abba tsaya da kafarka”.
Kamar yadda kowa ya sani ne tace fina-finai, rubuce-rubuce tare da waka na daya daga cikin manyan aiyukan da suka rataya akan Hukumar domin tabbatar da tsafta tare da dora komai a bisa doron doka da oda.