Nan Ba Da Jimawa a Matsalar Ruwa A Tudun Wada Za Ta Zo Karshe – Shugabar Karamar Hukumar

Date:

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo

 

Shugabar ƙaramar hukumar Tudun wada, Hajiya Sa’adatu Salisu Soja, ta bayyana cewa ta mika koken al’ummar karamar Hukumar Tudun wada ga Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, game da matsalar Ruwan famfo da ke damun al’ummar yankin.

Haj Sa’adatu ta ce baya ga matsalar ruwan za a magance matsalolin da rashin kammala titi mai tsawon kilometer 5 na karamar hukumar Tudun wada yake haifarwa ga al’umma.

Talla

Shugabar karamar hukumar ta bayyana hakan ne yayin da ta kai ziyarar gani da ido gidan Ruwa na karamar hukumar Tudun wada.

Ta kara da cewa ta kai wannan ziyara ne, domin ganin halin da gidan ruwan yake ciki da kuma matsalolin da suke damun gidan ruwan domin sanin ta yadda zaa a magance matsalolin.

Gwamnan Kano zai sauya wasu daga cikin kwamishinoninsa

“Wannan ziyara umarni ne daga mai girma Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da mu je da ma’aikata a gani me cece matsalar da tasa al’ummar Tudun wada basa samun ruwan sha?”. Inji Hajiya Sa’adatu Salisu

“Cikin ikon Allah ma’aikata har sun zo daga ma’aikatar aiyuka ta Jihar Kano, karkashin jagorancin kwamishinan aiyuka na jihar Kano domin duba halin da dükkan wannan gurare suke ciki”.

Ta kuma bada umarnin da a biya dukkan ma’aikatan wucin gadi (Temporary da Messengers) da aka dade ba’a biyan su hakkokinsu ba, kuma ta ce ashirye ta ke domin cigabada bijiro da managartan ayyukan da za su kawowa a’lummar karamar hukumar Tudun wada cigaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...