APC Kano: Martani, Budaddiyar Wasika Zuwa ga Shugaba Tinubu – Daga Maikudi Lawan

Date:

Daga Maikudi Lawan, PhD

 

Ya mai girma shugaban kasa kuma babban kwamandan Askarawan tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu GCFR, a madadin al’ummar jihar Kano da kuma daukacin ‘ya’yan jam’iyyarmu ta APC, musamman na shiyyar Kano ta tsakiya ina so in nuna matukar jin dadi da godiyarmu a gare ka bisa ga nadin da ka yi wa Rt—Hon—Yusuf Abdullahi Ata a matsayin karamin ministan ma’aikatar gidaje da raya birane ta kasa.

Ranka ya dade, nadin da aka yi wa Ata, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano wanda ya fito daga shiyyar Kano ta tsakiya, ba wai kawai daidaito ya kawo a siyasa jihar kano ba, har ma ya rage damuwar al’ummar Kano ta tsakiya.

Kafin nadin Ata, mu mutanen Kano ta tsakiya ba mu da isasshen wakilci a majalisar ministocin tarayyar Nigeriya, saboda manyan mukamai guda hudu da aka baiwa jiharmu duk an yiwa mutanen da suka fito ne daga yankin Kano ta Arewa.

Shugaban jam’iyyarmu ta APC na kasa Dr Abdullah Umar Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau I Jibrin da karamin ministan gidaje da raya birane Abdullahi Tijjani Muhammad da Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilai Rt Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bichi, duk sun fito ne daga shiyyar Kano ta Arewa.

Talla

A sakamakon haka, a lokacin da sanarwar nadin Hon. Ata a matsayin Minista ta fito da yake dan siyasa ne tun daga tushe talakawa, al’ummar Kano ta tsakiya da ta kunshi kananan hukumomi 15 wacce ake ganin ita ce shiyya mafi yawan kuri’u a jihar sun yi murna sosai, Wannan murna ba ta tsaya ga ’yan APC kadai ba ta yadu a sassa daban-daban da suka hada da ‘yan kasuwa, dalibai, mata, da malamai, har ma da magoya bayan jam’iyya mai mulki a jihar, NNPP.

Hasali ma, Sanatan NNPP mai wakiltar Kano ta tsakiya, Sanata Rufa’i Hanga, sai da ya fito fili ya goyi bayan nadin da aka yiwa Ata, inda ya bayyana shi a matsayin dan siyasa tun daga tushe kuma dan siyasa mai kishin kasa da al’umma,
Eh, ya koka bisa bazanar da kujerarsa ta samu, saboda Ata ya cike gibin da talakan Kano ta tsakiya suka samu a majalisar zartarwa tarayya.

Duk da wannan ci gaban da ya haifar da kalubale ga jam’iyyar NNPP, Amma wasu daga cikin wakilansu a cikin jam’iyyarmu ta APC suna yunkurin haifar da rashin jin dadi da yaudarar ka ta hanyar wata budaddiyar wasika da wani Yusuf Gogori ya rubuta.

Tun bayan nadin Ata, al’ummar Kano ta tsakiya, wadanda a da suke jin an yi watsi da su, sun dawo cikin harkokin siyasa. Yanzu suna Jin cewa suma an San da su kuma an san muhimmancinsu da rawar da zasu taka wajen kawo cigaba mai ma’ana.

Sabanin ikirarin baya, nadin Ata ya hada kan mu muda muke cikin jam’iyyar APC kuma zai ba mu damar kunkarar zaben 2027 mai zuwa wanda muke fatan yin nasara. Dukkanin ‘ya’yan jam’iyyar mu da suka hada da jagoranmu, shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, suna goyon bayan nadin da ka yiwa Ata, saboda sanin da suka yi masa na kishin jam’iyyarmu ta APC tun daga matakin jihar kano da kasa baki daya.

Tun bayan da jam’iyyarmu ta sha kaye a zaben gwamna da ya gabata, wani mutum daya da yake jibantar al’amuran jam’iyyar APC a Kano sai mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibrin, CFR, wanda yake marawa shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje baya, wajen kula da jam’iyyar APCn Kano.

Dalilin da ya sa Tinubu ya dage taron majalisar zartarwar kasa – Fadar Shugaban Kasa

Saboda abubun suka ga yana yi, dubban ‘yan jam’iyyar NNPP da suka hada da shugabanninta da mukarraban gwamnan jihar suna ta yin watsi da lafiyarsu ta jar hula suna ajiye jam’iyyarsu ta NNPP suna dawo wa jam’iyyar APC . Wanda hakan ya hana jagoran NNPP kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023, Eng Rabiu Musa Kwankwaso barci.

Sanata Barau, wanda ya taka rawar gani a yakin neman zabenka a Kano da Arewa, ya saukar da kansa wajen jiyar da al’ummarsa dadi tun dawowar dimokradiyya a 1999.

Ya kamata a lura da cewa, Barau ya shi ne mutum daya tilo da ya ci zaben dan majalisar tarayya a shiyyoyi biyu daban-daban. A shekarar 1999 ya wakilci karamar hukumar Tarauni ta Kano ta tsakiya, kuma ya wakilci mazabar Kano ta Arewa har sau uku daga 2015 zuwa yanzu.

A zaben da ya gabata, shi ne dan takarar Sanata daya tilo daga jam’iyyarmu ta APC da aka dawo da shi, wanda hakan ke nuna farin jininsa a tsakanin al’ummar shiyyar Kano ta Arewa da ta kunshin kananan hukumomi 13.

Ya mai girma shugaban kasa, mun gode da yadda ka magance rikice-rikice da aka iya tasowa saboda rashin baiwa shiyyar Kano ta tsaki kulawar da ta kamata, amma yanzu kowa a yankin yana Jin cewa an kasan da shi.

Ranka ya dade, muna godiya

Dr Maikudi Lawan, ne ya rubuto wasikar daga karamar hukumar Gwale Kano ta tsakiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...