Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake dage zaman majalisar zartarwa ta tarayya bayan rasuwar babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.
Shugaban ya bayyana cewa daga baya za a bayyana sabuwar ranar da za a gudanar da taron.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar.

Ya rubuta: “Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin dage taron majalisar zartarwa ta tarayya har zuwa wani lokaci da za a bayyana nan gaba.
Kotu ta hana CBN riƙe kuɗin ƙananan hukumomin Kano
Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin sassauta tutar Nigeriya zuwa Rabi har na tsahon Kwanaki 7 a duk fadin kasa saboda girmamawa ga Babban hafsan sojin.
Idan za a iya tunawa da safiyar wannan rana ce ta Laraba fadar shugaban kasar Nigeriya ta bayar da sanarwar mutuwar Taoreed Lagbaja babban hafsan sojin kasa na Nigeria.