Daga Isa Ahmad Getso
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin gudanar da bincike don gano abun da ya haifar da rashin jituwa tsakanin kwamishiniyar ma’aikatar jin kai Hajiya Amina HOD da wata likita dake aiki a asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake Kano.
Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.
Ya ce tuni ma’aikatar ta dauki matakan da suka dace don magance rashin fahimtar juna da ta faru tsakanin kwamishiniyar agajin jin kai Hajiya Amina HOD da wata likita a Asibitin kwararru na Murtala Mohammed Kano.

Ya ce Gwamna Abba Yusuf, ya umurci ma’aikatar da ta binciki lamarin tare da gabatar da cikakken Rahoton bincike ga ofishinsa cikin sa’o’i 48 kan ainihin abun da ya faru.
“Mun kafa wani kwamiti wanda zai binciki lamarin kuma za a warware matsalar cikin ruwan sanyi.”
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Kungiyar Likitocin Najeriya NMA, ta fitar da wata takarda zuwa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda ta bukaci ya tsige kwamishiniyar jin kai, Hajiya Amina HOD bisa zargin cin zarafin daya daga cikin mambobinsu a lokacin da yake bakin aiki a asibitin Murtala Mohammed.
Gwamnan Kano Ka Cire Kwamishiniyar Jin Kai Saboda Za ta Jawo Maka Bakin Jini – Anas Abba Dala
Kungiyar ta yi Allah wadai da cin zarafi da ake zargin kwamishiniyar ta yiwa wata Likitan da ke aiki a asibitin, inda ta bukaci a gaggauta korarta daga mukaminta.
Lamarin ya faru ne a ranar 1 ga Nuwamba, 2024, a sashin kula da lafiyar yara na gaggawa na asibitin kwararru na Murtala Muhammad, inda aka ce wanda abin ya shafa ita ka dai ce a bakin aiki.
NMA ta ce, “Abin takaici ne yadda kwamishiniyar a jihar Kano ta ci zarafin wata jami’a dake aikin ceto rayuwar al’ummar jihar.”
“Irin waɗannan ayyukan suna nuna rashin tausayi ga ƙwararrun kiwon lafiya da kuma yin watsi da ƙalubalen ɓangaren kiwon lafiya ke fuskanta, gami da ƙarancin ma’aikata, da matsalolin tsaro ga ma’aikatan kiwon lafiya.”
“kungiyar NMA ta yi kira da a gaggauta korar kwamishinan ayyukan jin kai, saboda rashin da’a da kuma rashin mutunta ka’idojin Mutane da ta yi.
Sai dai kwamishinan lafiya na jihar ya bayyana cewa an shawo kan lamarin kuma tuni sun gana da shugabannin kungiyar likitocin kuma nan ba da jimawa ba za a mika sakamakon binciken ga gwamna.