Allah Madaukakin Sarki ne yake ba da mulki ga wanda ya ga dama, kuma Shi kadai ne mai ikon karɓe shi a duk lokacin da Ya so, kuma babu wanda zai iya ƙalubalantar hakan – Alkur’ani – Sura Ta 3, Aya Ta 26.
Karanta rubutun Adnan Mukhtar a kan wannan batu zai sanya mutum ya tambayi kansa, ko marubucin da masu daukar nauyinsa suna kimanta rawar ƙaddara a harkokin ɗan’adam, da har za su yi irin waɗannan tunanin da suka yi a rubutun inda suka danganta samun shugabancin siyasa gaba ɗaya da dabaru ko wayon mutum.
Wataƙila ɗaukar aniyar ɓata sunan Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Jibrin Barau, ya sanya marubucin ya makance. Sai dai, da ya ɗan yi nazari, da zai iya tsira daga kunyata kansa kuma ya hana mu fadawa zarge-zarge da ƙage game da rikicin kujerar mulki da ya yi magana a kai, wanda mafi yawanci su ne tushen wannan tunanin nasa..

A sanina, duk mutanen da ya ambata a rubutunsa suna da nasarorinsu daga Allah su ke kuma ba za su yi ƙiyayya da kowa ba domin sun san cewa babu mutumin da zai hana wani abin da Allah Ya ba shi.
Bayan wannan, yana da kyau a yi bayani kan wasu abubuwan ƙage a cikin rubutun don kada ya yaudari jama’a, ko kuma ya shafa wa wasu shugabannin baƙin fenti.
Wanda ba shi da wayo ne kawai zai gaskata cewa Sanata Barau ne ke da hannu wajen cire Abdullahi T. Gwarzo a matsayin minista, kamar yadda marubucin ya yi ikirari, domin kowa ya san cewa nada minista da cire shi yana ga shugaban ƙasa ne.
Mun shaida yadda aka naɗa ministoci da kuma yadda shugabanni daban-daban suka cire su. Babu wanda ya danganta hakan ga wani sai shugaban da ke da alhaki na kolokuwa.
A wannan fuska, za mu iya tuna yadda Janar Abdulrahman Dambazzau ya zama minista a gwamantin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari amma daga baya aka maye gurbinsa da Janar Salihi Magashi. Haka kuma, Alhaji Sabo Nanono ya samu muƙami a karkashin Buhari, amma daga bisani aka cire shi daga mukamin nasa..
Haka kuma, za mu iya tuna batun Maryam Shetty wadda aka zabo don tantancewa a majalisar dattijai amma aka janye sunanta a minti na karshe. Haka ma, Jemila Salik da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada a watan Fabrairu na shekarar 2014, amma aka sauya sunan ta da Malam Ibrahim Shekarau kafin tabbatarwa. A dukkanin misalan nan, ba wanda ya danganta wadannan sauye-sauyen ga wani sai shugabannin kasar da suka zaɓi su yi aiki da wanda suka ga dama a bisa tsarin mulkin kasa.
Goyon bayan da aka yi wa nadin Hon. Yusuf Abdullahi Ata ba ya tsaya ga jam’iyyar APC kaɗai ba ne, saboda an yi shi ne bisa cancanta kuma don daidaita al’amuran siyasar Kano. Kowa ya yi mamaki a lokacin da Sanata Rufai Hanga (NNPP, Kano Ta Tsakiya) ya gaya wa duniya a majalisar dattijai cewa nadin Ata ya kayatar da shi, kuma ya bayyana shi a matsayin jigon siyasa kuma mai ƙwarewa a harkar.
Sanata Barau mutum ne mai tawali’u, mai girmama mutane kuma mai kyakkyawar zuciya; waɗannan halayen sun sa shi ya shiga cikin al’ummomi mabukata, ‘yan kasuwa, masu sana’ar hannu, manoma, mata, matasa, da malaman addini a Kano da wajenta.
Ogan Boye ya kafa kwamitin farfado da kudin haraji a karamar hukumar Nasarawa
Abu ne sananne cewa tun lokacin da ya fara harkar siyasa, ya ci gaba da tsayawa kan nagarta ba tare da rikici, gaba ko ƙiyayya ba ga wasu. Wannan shi ne abin da ya keɓanta da shi kuma watakila shi ne abin da ke hana Mukhtar da masu ɗaukar nauyinsa barci.
Ko mai lura da al’amura na yau da kullum na siyasar Kano ya san cewa babban burin Sanata Barau shi ne ya bauta wa jama’a da inganta rayuwar talakawa. Ya yi wannan aiki sosai ta hanyar ayyukan ci gaban kayayyakin more rayuwa, ilimi, lafiya, aikin gona, wutar lantarki da sauransu, tare da dokoki masu inganci da haɗuwa da mutane.
‘Yan siyasa kaɗan ne a Kano za su iya kai matakin mataimakin shugaban majalisa, wanda ya shafi rayuwar mutane tun lokacin da yake wakili a majalisar wakilai zuwa lokacin da ya zama kwamishina, sanata, kuma yanzu mataimakin shugaban majalisar dattijai.
Shi ya sa mutane da yawa ke sauya sheka zuwa APC a Kano, ba don dalilai na kudi ba, kamar yadda marubucin ya ƙirƙira, duk da ƙoƙarin ɓata waɗannan nasarorin daga wasu jam’iyyun siyasa ta hanyar ɗaukar wasu mutane su yi ikirarin ƙarya, ba za a iya musanta nasarar Sanata Barau wajen kawo ci gaba mai yawa ga Kano ba, ba iya Kano ba, har ma da duk yankin Arewa maso Yamma.
Cire T-Gwarzo Daga Minista Babban Kuskure ne – Kungiya Matasan APC ta Kasa
Nuna cewa mutane suna canzawa zuwa gare shi domin abin da za su samu daga gare shi alama ce tsoro. Duk da haka, Sanata Barau bai damu ba, yana sane da cewa Kano jihar APC ce da ta samu wani ƙanƙanin koma-baya a 2023 amma za a sauya.
Bugu da ƙari, mutanen Kano za su zaɓi wanda zai jagorance su a 2027 bisa ga abin da suka vani na waɗanda aka gabatar da su ba bisa son zuciyar wasu ba, wadanda za su iya sadaukar da nagartarsu saboda ribar kansu.
Kano ta zabi Rabiu Musa Kwankwaso daga Kano Ta Tsakiya a 1999, Malam Ibrahim Shekarau daga wannan yankin tsawon wa’adi biyu a jere, sannan ta sake zabar Kwankwaso na tsawon shekaru huɗu, ma’ana, ta ba wa yankin shekara 16.
Wadannan al’umma su ne dai waɗanda za su sake yanke hukunci kan abin da ya fi dacewa da su a 2027 kuma ba za su bari a yaudare su su sadaukar da nagarta domin faranta wa wasu kaɗan masu son kai rai ba. Allah SWT zai kunyatar da Mukhtar da masu ɗaukar nauyinsa lokacin da Barau zai zama gwamnan jiharmu ta Kano mai albarka, in sha Allah, nan da 2027.
Amin Ya Allah.