Gwamna Kano ya Magantu kan yaran da aka kai Kotu bisa zargin shiga zanga-zanga

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

Gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin yin duk mai yiwuwa don ganin ya dawo da yaran kano da aka kai su Kotu a Abuja bisa zarginsu da shiga zanga-zangar tsadar rayuwa.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito an gudanar da Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a duk fadin Nigeria a ranar 1 ga watan Ugusta da ya gabata.

Yayin zanga-zanga yan sanda sun kama Matasa da dama musamman wadanda suka rika daga tutar kasar Rasha, wanda hakan tasa a ranar juma’ar nan aka gurfanar da su a gaban wata kotu dake Abuja.

Talla

Yanayin da aka nuna yaran lokacin da suka shiga cikin kotun ya tayar da hankulan al’umma musamman yan Arewacin Nigeria, saboda ana ganin mafi yawan yaran an Kamo su ne daga jihohin Arewacin Nigeria musamman Kano.

Hakan tasa al’umma suke ta kiraye-kiraye musamman ga shugabanni Arewacin Nigeria da su sanya baki a sako yaran kasancewarsu kananan yara kuma duk an barsu cikin yunwa da kaskananci.

Martani: Tsari da Ingancin Siyasar Sanata Barau

A daren jiya juma’a gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nuna rashin jin dadinsa da halin da yaran suke cikin.

A wani rubutu da ya gwamnan ya wallafa a sashin shafinsa na Facebook ya an jawo hankalin Kan batun yaran, Inda yace tuni ya umarci babban lauyan jihar kano kuma kwamishinan Shari’ar da yayi duk abun da ya kamata domin karɓo yaran da suke yan Kano a cikin su.

Al’ummar dai yana ta kiraye-kirayen ya kamata shugabannin arewa su dauki matakan da suka dace domin ganin ba a cigaba da rike yarana ana azabtar da su ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...