Daga Abubakar Isa
Shugaban karamar hukumar Nassarawa Amb. Imam Yusuf ya kaddamar da wani sabon kwamitin da zai ba da sharar yadda za a inganta Kudaden haraji a karamar hukumar don cigaban al’umma.
A cikin wata sanarwa da daraktan harkokin mulki na karamar hukumar Nasarawa Auwal Yunusa Makama ya sanyawa hannu ya ce shugaban karamar hukumar ya samar da kwamitin ne domin inganta hanyoyin samar da Kudaden haraji don samawa matasan yankin aiyukan yi.

Amb. Yusuf Imam ya ce an samar da yan kwamitin ne bisa chanchanta a don haka ya bukaci su da su yi aiki tukuru don sauke nauyin da aka dora musu.
Ga sunayen yan kwamitin kamar haka:
1. Dr Bello Abdull Isa T/Murtala – Shugaba
2. Dr Mustapha Usman Baba K/Goje – Mataimakin shugaba
Ma’aikatan shara a kano sun zargi Danzago da hana su Albashinsu na watanni 6
3. Barrister Umar Shehu Kwaji – Sakatare
4. Barr. Ibrahim Isa Matawalle Gwagwarwa – Mamba
5. Amb. Jamilu Bala Gama – Mamba
6. Hon Kamal IG Kawaji – Mamba
7. Muhamma Adam Bomboy Gama – Mamba