T- Gwarzo ya aikawa Sabon ministan Gidaje Yusuf Abdullahi Ata muhimmin sako

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Tsohon karamin Ministan gidaje da raya burane Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ya sha alwashin baiwa sabon ministan da ya gaje shi Yusuf Abdullahi Ata duk wata gudunnawa da ta dace domin ya sami nasarar sauke nauyin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dora masa.

“Ina baka tabbacin zan baka duk wata gudunnawa da kake bukata daga gare ni domin cigaban ma’aikatar da Nigeria baki daya”.

Talla

Abdullahi Tijjani Gwarzo ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya wallafa a sahihin shafinsa na Facebook na taya Ata murnar tantance shi da majalisar dattawa ta yi a jiya laraba domin kasamcewa ministan Gidaje kuma dan majalisar zartarwa ta kasa.

” Ina baka shawarar ka hada kai da Babban ministan wannan ma’aikata wato Arc. Ahmad Musa Dangiwa domin ku yi aiki tare domin tabbatar da kudirin shugaban kasa Bola Tinubu na inganta harkokin gidaje da raya burane a Nigeriya”.

Ma’aikatan shara a kano sun zargi Danzago da hana su Albashinsu na watanni 6

T Gwarzo ya kuma ta ya Yusuf Abdullahi Ata murna da majalisar dattawa ta tantance shi kuma ta amince da nadin da Shugaba Tinubu ya yi masa a matsayin ministansa.

Ya yi fatan sabon ministan zai yi aiki cikin kwanciyar hankali kuma ya gama lafiya ba tare da wata matsala ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...