Jinkirin isar kayan zaɓe da ma’aikata ya haifar da tsaiko a zaɓen ƙananan hukumomin Jihar Kaduna da ke gudana a ranar Asabar.
An shirya fara zaɓen ne da misalin ƙarfe 8 na safe, amma har bayan ƙarfe 10 na safe, ba a fara kaɗa ƙuri’a ba a mafi yawan rumfunan zabe.
Wakilinmu da ya ziyarci wurare da dama a unguwannin Tudun Wada Badiko da Magajin Gari da Unguwar Sarki, inda ya lura cewa ba a kai kayan zaɓe zuwa rumfunan zaɓe ba.
An tsara fara yin rijista da kaɗa kuri’a da misalin ƙarfe 8:30 na safe kuma a kammala da ƙarfe 2 na rana.
Kotu ta ki amincewa da umarnin dakatar da zaben kananan hukumomin Kano
Tsohon Kansila na Unguwar Sarki, Zubairu Shan’una, ya ce, “Har yanzu muna nan muna jiran kayan zaɓe su iso.
“Kamar yadda ka sani, zaɓen ya kamata ya fara da ƙarfe 8:30 na safe, amma har ƙarfe 10 na safe kayan zaɓe ba su iso Unguwar Sarki ba,” in ji shi.
Malam Idris, wakilin jam’iyya a rumfar zaɓe ta Makarantar Sakandare ta Maimuna Gwarzo da ke Tudun Wada, ya ce ya isa wajen zaɓen da misalin ƙarfe 6:30 na safe.
Amma a cewarsa ma’aikatan zaɓen ba su isa wajen ba, kuma ba a raba kayan zaɓe ba.
A Magajin Gari, an samu rikici yayin da wakilan jam’iyyu suka yi ƙorafin samun jinkirin rabon kayan zaɓe.