Tinubu ya buƙaci CAF ta ɗauki mataki kan Libya

Date:

 

 

Shugaban ƙasan Najeriya Bola Tinubu ya yi wa ƴanwasan tawagar Super Eagles maraba da dawowa Najeriya bayan matsalar da suka fuskanta, sannan ya buƙaci a gaggauta bincike, tare da tabbatar da hukunci na adalci game da tirka-tirkar da ta faru da ƴanwasan Super Eagles a Libya.

Tinubu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai shi shawara na musamman kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ya fitar.

Talla

Tinubu ta buƙaci kwamitin ladabtarwa na CAF, “ta yi bincike, sannan ta bayar da shawarwarin irin hukuncin da ya kamata a ɗauka a kan waɗanda suka saɓa ƙa’idoji da dokokin hukumar.”

Da dumi-dumi: Nijeriya ta gayyaci jakadan Libya kan batun Super Eagles

Shugaban ya kuma yaba da ƙoƙarin ma’aikatar harkokin ƙasashen waje da ma’aikatar wasanni bisa ƙoƙarin da suka yi wajen shawo kan lamarin.

Haka kuma ya yaba da juriyar da ƴanwasan suka nuna duk da matsalar da suka fuskanta.

Talla

A ƙarshe ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon ƙafa da su yi duk mai yiwuwa domin hana sake aukuwar irin wannan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...