Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta gayyaci jakadan kasar Libya a Nijeriya biyo bayan cin zarafin tawagar Super Eagles a Libya bayan an karkatar da jirginsu ba zato ba tsammani.
Leadership ta rawaito cewa ministan Harkokin Waje na Nijeriya, Yusuf Tuggar, ya tabbatarwa da manema labarai na fadar gwamnati cewa, a yanzu haka ana kokarin dawo da tawagar kwallon kafa ta kasa Najeriya.
Adadin yaran da ke fama da yunwa ya karu a Arewacin Nigeria – Bincike
Tuggar ya bayyana cewa hukumomin Najeriya suna tuntubar tawagar Super Eagles kai tsaye, sannan jami’an ofishin jakadancin Nijeriya da ke Libya sun tura jami’ai don su taimaka wa ‘yan wasan da jami’an da suka makale.
Ya kara da cewa ana daukar lamarin da matukar mahimmanci.