Zargin almundahana: Hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano na bincike kan shirin tura ɗalibai karatu ƙasar waje

Date:

 

 

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta fara bincike kan zargin almundahana a tallafin karatu na ƙasashen waje da aka tura daliban jihar domin karo karatu.

Hukumar tana yi wa manyan jami’an ma’aikatar ilimi mai zurfi na jihar tambayoyi game da batun dalibai 1,001 da ake ikirarin suna karatu a Indiya da Uganda.

Talla

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa gwamnatin jihar ta ɗauki nauyin dalibai 1,001 masu neman digiri na biyu don yin karatu a Indiya da Uganda.

Shirin yana cikin tsare-tsaren tallafin karatu na kasashen waje wanda gwamna Abba Yusuf ya ƙaddamar.

Kwanan nan, Yusuf ya shirya liyafar bankwana ga rukunin farko na dalibai 550 da suka ci gajiyar tallafin a gidan gwamnati, inda ya jinjina wa tsohon gwamna Rabi’u Kwankwaso kan kirkiro shirin.

Sai dai NAN ya samu labarin cewa ɗalibai 418 ne kawai aka tura zuwa kasashen waje don karatu, wanda ya haifar da tambayoyi kan inda sauran ɗaliban suke.

Gwamnan Kano ya bada tallafin Naira miliyan 100 ga wadanda gobarar kasuwar kantin kwari ta shafa

Da aka tuntube shi, jami’in hulda da jama’a na hukumar, Kabiru A. Kabiru, ya tabbatar da rahoton, yana mai cewa an yi wa manyan jami’ai biyu tambayoyi kan zargin almundahana ta tallafin karatu.

Ya ce ana gudanar da bincike don gano waɗanda ke da alhakin zargin damfarar da kuma hukunta su.

Talla

“Binciken farko ya gano ayyukan almundahana a ofishin ma’aikatar ilimi mai zurfi kan daliban da aka tura don neman digiri na biyu a Indiya da Uganda.

“Mun buɗe bincike don gano gaskiyar lamarin. Duk wanda aka samu da hannu a ciki, za a gurfanar da shi, ba tare da la’akari da matsayin sa ba,” inji Kabiru. (NAN)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...