Ya zama wajibi Tinubu ta dawo da tallafin man fetur – Peter Obi

Date:

 

 

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya soki Shugaba Bola Tinubu kan ƙara farashin man fetur din da ya yi, yayin da yake hutu.

Obi ya nuna damuwarsa kan yadda Tinubu ya bari Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL), ya ƙara farashin mai ba tare da wata sanarwa ba, wanda hakan ya ƙara jefa ’yan Najeriya cikin matsin tattalin arziƙi.

 

Talla

A yayin da Shugaba Tinubu ke hutu a ƙasar Faransa, NNPCL ya ƙara farashin man fetur a faɗin Najeriya, inda a wasu yankuna farashin ya kai har Naira 1,075 kan kowace lita.

Jama’a da dama sun nuna rashin jin daɗinsu, wanda hakan ya sa suka yi kira ga Tinubu ya janye ƙarin da aka yi wa man fetur.

Sai dai gwamnatin tarayya ta hannun Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ta ce NNPCL ne ya yi ƙarin babu hannunta a ciki.

Zargin almundahana: Hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano na bincike kan shirin tura ɗalibai karatu ƙasar waje

Obi, ya wallafa a shafukan sada zumuntarsa cewar, gazawar gwamnati wajen tsara yadda za a tafiyar da albarkatun ƙasa na ƙara taɓarɓarewar tattalin arziƙi.

Ya yi zargin cewa ƙarin farashin ya nuna rashin tausayi da kuma rashin kyakkyawan shiri na tattalin arziƙi, haka kuma akwai ruɗani game da ayyukan da NNPCL ke gudanarwa.

Obi, ya ƙara da cewa tun da Shugaban ƙasa shi ne Ministan Man Fetur, yana da alhakin kula da NNPCL da hukumomin da ke sa ido a kan kamfanin.

A cewarsa ya zama dole ga Shugaba Tinubu ya nemo mafita kuma ya janye ƙarin farashin, musamman ganin yanayin wahalar da ’yan Najeriya ke ciki.

Haka kuma, Obi ya soki Tinubu kan yanke irin wannan shawara mai tsauri yayin da yake tsaka da yin hutu.

Talla

Ya bayyana cewar hakan yana nuna rashin tausayi da damuwar da ’yan ƙasa za su shiga.

Kalaman Obi na zuwa ne bayan da tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki Tinubu kan jefa ‘yan Najeriya cikin wahala ta hanyar ƙara farashin man fetur.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...