Daga Sadiya Abubakar
Babu alamu kawo karshen rikicin jam’iyyar adawa ta PDP yayin da wani bangare na shugabancin jam’iyyar na kasa ya dakatar da Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Umar Damagum, da Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Samuel Anyanwu, bisa zargin rashin biyayya ga jam’iyyar.
Tun da farko, wani bangare na shugabancin jam’iyyar na kasa da ke goyon bayan Damagum ya sanar da dakatar da Mai Ba da Shawara Kan Harkokin Shari’a na Kasa, Kamaldeen Ajibade, da Sakataren Yada Labarai na Kasa, Debo Ologunagba, bisa zargin rashin biyayya ga jam’iyyar.

A sabon yanayi, Ologunagba, a cikin wata sanarwa ranar Juma’a, ya kuma sanar da dakatar da Damagum da Anyanwu.
Sanarwar ta ce , “Shugabanci na kasa na jam’iyyar PDP ya yi la’akari sosai da jerin korafe-korafen da aka gabatar kan Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Amb. Iliya Damagum da Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Sanata Samuel Anyanwu, musamman dangane da wasikar da suka aike wa Kotun Daukaka Kara a kara mai lamba: CA/PH/307/2024 da ke kalubalantar matsayar jam’iyyar a kan batun tsoffin ’yan majalisar dokokin jihar Ribas guda 27 da suka fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
Sabon Rikici ya balle tsakanin yan majalisar tarayya na jam’iyyar NNPP a Kano
“Shugabancun jam’iyya na kasa ya yi Alla wadai da wannan abin da ya saba wa jam’iyya da suka aikata, wanda ya saba wa kundin tsarin mulkin PDP (wanda aka yi wa gyaran fuska a shekarar 2017) da kuma rantsuwar da suka dauka a ofis.

“Saboda haka, shugabancin jam’iyya bisa ga sashe na 57, 58 da 59 na kundin tsarin mulkin PDP, ta dakatar da Amb. Illiya Damagum da Sanata Samuel Anyanwu daga mukamansu na Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar na Kasa da Sakataren Jam’iyyar na Kasa, kuma ta tura su zuwa Kwamitin Ladabtarwa na Kasa domin ci gaba da daukar mataki.
“A halin yanzu, an dakatar da wadannan jami’ai daga duk wani taro, ayyuka da shirye-shiryen NWC har sai an kammala binciken da Kwamitin Ladabtarwa na Kasa zai yi.”