Daga Rukayya Abdullahi Maida
Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane, Abdullahi Tijjani Gwarzo, ya taya shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu GCFR da daukacin ‘yan Najeriya murnar cikar kasar shekaru 64 da samun ‘yancin kai.
Ministan ya bayyana hakan ne a wani sako da ya aikewa ‘yan Najeriya na bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kai ta bana, wadda mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Adamu Abdullahi ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.

Ya ce yayin da Nigeria ke cika shekara 64 da samun ‘yancin kai, ‘yan Najeriya na da dalili yin murnar nasarorin da aka samu tsahon Shekaru 64.
“Duk da cewa kasancewar a matsayin kasa mun yi tafiya mai tsauri kuma mai sarkakiya, amma da jajircewar shugabanninmu, Najeriya ta samu gagarumin ci gaba a matsayinta na kasa mafi karfin tattalin arziki da dimokuradiyya a nahiyar Afirka”, in ji Ministan.
Yancin kai: Muhimman bangarori 6 na jawabin shugaban ƙasa Bola Tinubu
Ministan ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, yana bakin kokarinsa wajen gyara matsalolin kasar, yana mai cewa an bullo da tsare-tsare kuma an bullo da ayyuka da dama kuma ya himmatu don magance matsaloli da dama da kasar ke fuskanta.
Minista Gwarzo, ya bayyana cewa ma’aikatarsu ta gidaje da raya birane tana ci gaba da gudanar da shirin gina gidaje na “sabunta fata” da nufin tabbatar da cewa kowane mutum ya samu gida mai aminci, mai araha, mai daraja ba tare da la’akari da jinsi ko matsayi ba.

Don haka Ministan ya yabawa ‘yan Najeriya bisa yadda suke baiwa cigaban dimokaradiyya goyon bayan a ƙasar nan, ya mai cewa nan da yan shekaru masu zuwa ƙasar nan zata abar alfahari a karkashin gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu.