Daga Mustapha Ibrahim
Babbar kotun tarayya mai zamanta Kano karkashin jagorancin Mai Shari’a S. A Amobeda ta baiwa hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano wato KANSIEC umarnin dakatar da duk wasu shirye-shirye gudanar da zaben kananan hukumomin jihar da ta shirya yi a watan gobe.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito hukumar zaben ta KANSIEC ta shirya gudanar da zaben kananan hukumomin jihar kano a ranar 26 ga watan October mai zuwa.

Wani Hon. Aminu Aliyu Tiga da jam’iyyar APC ne suka shigar da karar tare da neman kotun da ta dakatar da zaben har sai ta saurari kundarin Shari’ar.
A karar da suka shigar sun kalubalanci hukumar zaben Kano kan taka ƙa’idojin shirin gudanar da zaɓe da kuma sanya kudin siyan fom ɗin shiga zaɓe, wanda APC ta hannun Hon. AA Tiga yace bai gamsu da yadda aka shirya shiga zaben ba.
El-Rufa’i ya magantu kan dawo da Sarki Sanusi II gadon sarautar Kano
Kotun ta bada umarnin dakatar da duk wani shiri na shiga zaɓen har sai an fara shari’ar.
Kotun ta kuma ce zata fara sauraren karar ne a ranar 04 ga watan October mai kamawa.