Wani jirgin sama mallakar Saudi Airlines na ƙasar saudiyya ya da ya ɓace da fasinjoji kusan 300 ƴan Najeriya ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, bayan shafe sama da awanni 10 da tasowarsa.
Freedom Radio ta rawaito Jirgin ƙirar Boeing 777-300 mai lamba SV 0401 ya taso daga filin jirgin sama na Sarki Abdul’aziz da ke Jidda da misalin ƙarfe 10 da rabi na safiyar ranar wanda ake sa ran zai sauka Kano da ƙarfe 2 na rana, amma hakan bai samu ba.

Bayan awanni 3 da tashin jirgin ne, sai ya ɓace daga manhajar da ake bibiyar zirga-zirgar jiragen sama, lamarin da ya jefa iyalai da ƴan uwan fasinjojin cikin zullumi.
To sai dai jirgin ya samu sauka a Kano da ƙarfe 8:30 na daren Talata.
Jami’an jirgin sun sanarwa da fasinjoji cewa, jirgin ya sauka ne a Habasha domin rashin lafiya wani daga fasinjoji.

Sai dai wasu fasinjojin da Freedom Radio ta tuntuba sun ce, jirgin lalacewa yayi domin a inda aka sauke su, an shafe awanni biyar Injiniyoyi na ta aiki a kansa.