Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yabawa Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf kan dawo da Muhammadu Sanusi na II kan karagar mulkin Kano.
El-Rufai, ya ce dawo da Sarkin na daya daga cikin “Abubuwa mafiya muhimmaci da suka faru a rayuwat”.

Tsohon Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau Laraba, a yayin taron horas da matasa kan fasahar zamani na jihohin Arewa mai suna Arewa Tech Fest dake gudana a Kano.
Rasuwar yan sandan Kano babban rashi ne ga Nigeriya – Sarki Aminu Bayero
Taron ya samu halartar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf wanda ya samu wakilcin mataimakinsa da Gwamnan Katsina, Dikko Radda da wakilcin Gwamnan Zamfara.