Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima wanda ya wakilci shugaba Tinubu, a yayin jawabi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya, ya nemi da a yafewa Najeriya da sauran ƙasashe masu tasowa basukan da ake bin su.
“…dole ne mu tabbatar cewa duk wani gyara da za a yi wa tsarin kuɗaɗe na duniya da suka haɗa da cikakken tsarin yafe bashi…domin ƙasashe ƙanana da masu tasowa ba za su iya samun cikakken cigaban tattalin arziƙi ba ba tare da yin duba da sake nazari kan irin nauyin bashin da ke kansu.” In ji Kashim Shettima.
Sauran batutuwan da mataimakin shugaban ya taɓo a jawabin nasa sun haɗa da neman haɗin kan Majalisar Ɗinkin Duniya wajen ganin an mayar da kuɗaɗen sata da waɗanda aka fitar da su zuwa manyan ƙasashe ba bisa ƙa’ida ga ƙasashen da aka sato su.
Sanata Kashim Shettima ya kuma nemi zauren Majalisar da ya bai wa nahiyar Afirka da Najeriya gurbi a kwamitin tsaro na Majalisar ta Ɗinkin Duniya.

Me ya sa Najeriya ke son a yafe mata bashi?
“Yanzu haka nauyin bashin da ke kan Najeriya ya sa tana biyan fiye da kaso 70 na kuɗaɗen shigarta sannan ɗan abin da ya rage shugabanni na almubazzaranci da su. Wannan ne ya sa ƙasashe irin su Najeriya ke son a yafe musu bashi.”In ji wani masanin tattalin arziƙi kuma malami a kwalejin fasaha ta Kano, Malam Lawal Habib Yahaya.
Ya ce duk da shi bashi hanji ne domin babu ƙasar da ba ta cin bashi amma akwai yanayin da yake zamowa wasu ba alkairi ba.

“Matsalar bashi irin na ƙasashen Afirka kamar Najeriya shi ne yadda idan an ciwo bashin ba a amfani da shi yadda zai samar da cigaba da kuɗin shiga da ake buƙata da zai bai wa ƙasar damar biyan bashin ba tare da ji a jikinta ba. Akwai kuma matsalar rashawa da cin hanci.”
Dangane kuma da yadda ake biyan bashin, Malam Yahaya ya ce ” shi bashi irin wannan yana da abin da ake kira “compound interest” wato ribar da ke ruɓanyawa. Kenan ƙasa za ta iya biyan abin da ya nunka haƙiƙanin bashin saboda riɓanyar da yake yi.
Masana dai na alaƙanta wahalhalun da ƴan Najeriya ke ciki sakamakon cire tallafin mai da na wutar lantarki da ma na jami’o’i da alamu ke nuna ana shirin cirewa a nan gaba da ƙokarin da gwamnatin Najeriyar wajen tattara kuɗaɗe domin biyan basukan da ake bin ta.

Nawa ne basukan da ake bin Najeriya?
Wasu alƙaluma da Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya, NBS ta fitar waɗanda ta laƙanto daga hukumar da ke kula da basuka ta Najeriya sun nuna cewa ya zuwa watan Maris na 2024 Najeriya na da basuka a kanta na naira tiriliyan 121.67 kwatankwacin dalar Amurka 91.46.
Ƙididdigar ta nuna cewa daga cikin naira tiriliyan 121.67, naira tirilyan 56.02 basuka ne da Najeriyar ta ciyo daga waje, inda kuma gwamnatin tarayya ita kaɗai ta ciyo bashin naira tiriliyan 46.290.28 – fiye da kasafin kuɗin ƙasar na shekara biyu.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa bankin duniya na shirin bai wa Najeriyar bashin kuɗi har dala biliyan ɗaya da miliyan ɗari baƙwai ($1.7bn)