Yan sa-kai sun hallaka Ƙasurgumin dan ta’adda a jihar Zamfara

Date:

 

Rahotanni na nuna cewa an kashe ƙasurgumin ɗanbindiga, Kachalla Sani Black a Zamfara.

Ƴan sa-kai ne suka fafata da ɗanbindigar, suka kashe shi, suka ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, da wasu ƙudade.

Kafar PRNigeria ta ruwaito cewa bayan kashe ɗanbindigar, an kuma kashe ƴaƴansa biyu a fafatawar da aka yi a yankin Magama Mai Rake da ke ƙaramar hukumar Maru da ke jihar Zamfara.

Talla
Talla

Kachalla Sani Black fitaccen ɗanbindiga ne da ya addabi yankin Chabi da Ɗan Sadau a ƙaramar hukumar Maru da wasu yankuna na arewacin Zamfara da Kaduna da Neja da Kebbi.

Rahotanni sun ce yana da daba mai yawa da suka haura 150, sannan kuma a dabarsa a kan samu labarin yi wa mata fyade bayan an yi garkuwa da su.

Muhimmiyar sanarwa daga gwamantin jihar kano ga wadanda suka yi takara a NNPP

A wani labarin kuma, rikicin cikin gida ya ci wani fitaccen ɗanbindigar mai suna Kachalla Tukur Sharme a Kaduna.

Sharme ya mutu ne a sanadiyar rigimar da ta ɓarke a tsakanin dabarsa da wata dabar a wani waje da ake kira ‘Hambakko’ da ke tsakanin dajin Rijana da dajin Kaso, wadda ta yi sanadiyar tserewar wasu wadanda aka yi garkuwa da su.

Talla

A wata sanarwa da Kwamishinan Harkokin Cikin Gida na Kaduna Samuel Aruwan ya fitar, ya ce Sharme na ya jagoranci sace ɗaliban makarantar Bethel Baptist High School da ke Kaduna su 121.

Sharme ya daɗa yana addabar yankin Rijana da Kasarami da Jaka da-Rabi da Millenium City da Maraban Rido da Kujama da sauran garuruwan Jihar Kaduna.

Sanarwat ta ƙara da cewa wasu ƴanbindigar sun ji rauni a fafatawar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gyaran tarbiya: Makarantun Islamiyya na taka muhimmiyar rawar gani

Daga Zakariyya Adam Jugirya   Wani Malamin addinin musulunci a Kano...

Fadar shugaban ƙasa ta mayar da martani ga Kalaman Kwankwaso

Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta zargin Sanata Rabiu Musa...

Yadda Kwamishina a gwamnatin Kano ya tsayawa wani dilan ƙwaya aka bada belin sa a kotu

  Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Namadi, ya tsaya...

Kwankwaso ya caccaki gwamnatin Tinubu

  Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya...