Ibtila’in Ambaliyar Ruwa: Maryam Abacha Ta Jajantawa Al’ummar Maiduguri, ta nemi yan Nijeriya su kai musu dauki

Date:

 

Hajiya (Dr) Maryam Sani Abacha, Uwargidan tsohon shugaban Nijeriya, Marigayi Sani Abacha ta jajantawa al’ummar Maiduguri bisa ibtila’in ambaliyar ruwa da aka samu. Inda ta yi kira ga al’ummar Nijeriya da su tallafawa al’ummar Maiduguri da duk abin da Allah ya hore musu domin rage musu radadi.

“Ina jaje ga Nijeriya baki daya. Ina jaje ma al’ummar Borno. Borno gari na ne kuma mutane na ne. Iyayena duka daga Borno suke, don haka al’amarin ya shafi ni sosai kuma na damu matukar da faruwar Iftila’in”. Inji Maryam Abacha

Tinubu ya fi ƙarfin satar dukiyar Najeriya — Minista

Ta ci gaba da cewa, “Kuma magana da yawa da dangin mamana. Ko da safen nan mun yi magana kan yadda za a canza musu muhalli saboda Unguwarsu ruwa ya cinye. Da kuma yadda za a tallafa a kan abinci da kudi da sauran su. Da ni da yarana mun zauna akan abubuwan da mu ma za mu tallafa ma mutanen Maiduguri. Ta yadda inda kowa ya kawo kadan-kadan za a samu a yawa”, a cewarta

Ta kara da cewa; “ina jaje na wannan ambaliyar ruwa. Lokacin maigida an yi irin wannan ambaliyar ruwa, kuma ya bayar da taimako. Yanzu wajen shekara 30 ke nan”.

 

Hajiya Maryam Abacha ta yi kira da a yi kokarin gyara wannan dam din domin kaucewa aukuwar hakan a gaba, inda ta ce; “ya kamata a yi kokari a gyara wannan dam din. Saboda gobe ka da ya auku haka nan. Mu kasarmu gaskiya muna da sakaci, muna da kunci”.

Maulidi: Minista T Gwarzo ya bukaci al’ummar Musulmi su rika koyi da halayen Annabi S A W

Ta nemi da kowa ya zo ya bayar da na shi tallafin da taimako; “duk abin da za a taimaki al’umma a yi, a rika taimako. Ubangiji Allah ya kare gaba. Allah yasa kaffara a gare su mutanen Maiduguri. Allah yasa wannan ruwa ya zama alheri. Allah yasa ya wanke wannan jinin da Boko Haram suka zubar a Maiduguri.

Hajiya Maryam ta karkare da cewa; “ina kira ga ‘yan Nijeriya kowa ya kawo dauki, da mai yawa da kadan. Da kadan-kadan sai ya yi yawa, a kawo mutanen Maiduguri dauki. Allah ya taimaki Nijeriya.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...