Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya sanar da cewa farashin man fetur, na iya tashi sama da N1,000 kowace lita a gidajen Mai.
A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, Kamfanin NNPC Ltd ya fitar da kiyasin farashin man fetur (wanda aka samo daga matatar Dangote akan farashin watan Satumba na 2024) a fadin kasar.
Da dumi-dumi: NNPC ya bayyana farashin da ya sayi Man fetur din Ɗangote
Sanarwar ta bayyana farashin man kamar haka Legas, N950 kowace lita; Sokoto, N992 kowace lita; Oyo, N960 kowace lita; Kano, N999 kowace lita; Kaduna, N999 kowace lita; FCT, N992 kowace lita; Rivers, N980 kowace lita; da Borno, N1019 kowace lita.
Kamfanin ya ce bisa tanadin dokar masana’antar man fetur (PIA), ba gwamnati ce ta kayyade farashin man fetur din ba, sai dai ana tattaunawa kai tsaye tsakanin bangarorin da abun ya shafa.
YANZU-YANZU: Obasanjo Ya Isa Minna, Domin Gana wa da IBB, Abdulsalami, Gusau
“ NNPC ta tabbatar da cewa ta sayo kashin farko na man a matatar Dangote da dalar Amurka, Sannan ta ce zai fara siyan man da Naira ne daga ranar 1 ga Oktoba, 2024.
Hukumar NNPC ta bayar da tabbacin cewa idan aka sami ragen kudin man ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen ragewa kuɗin ga yan kasa don su sami sauki.