Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya isa Minna, babban birnin jihar Neja a yammacin Lahadin nan, kuma ya nufi gidan tsohon shugaban kasa na mulkin soja Ibrahim Badamasi Babangida (IBB).
Majiyoyin kadaura24 sun nuna cewa Obasanjo ya isa Minna ne da misalin karfe 4:15 na rana a cikin wani jirgi , inda ya taho daga birnin Benin inda ya je domin yi wa Esama na Masarautar Benin, Cif Gabriel Osawaru Igbinedion murnar cika shekaru 90 a duniya.
Abubunwan da ya kamata ku sani game da farashi da fitar da man fetur din Ɗangote
Rahotanni sun nuna cewa, tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar (rtd) da kuma tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Janar Aliyu Gusau (rtd), sum suna gidan na IBB domin jiran tsohon shugaban ƙasar Obasanjo.