Gwamnatin Kano ta dakatar da tsawaita wa’adin ma’aikata 4,000 da Ganduje ya yi

Date:

Aƙalla ma’aikatan jihar Kano 4,000 da gwamnatin tsohon gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ta tsawaita wa wa’adin aikinsu ne ake sa ran za su yi ritaya a ranar 1 ga Disamban 2024.

Gwamnatin jihar ta ce ta kammala bincike da tantace ma’aikatan, waɗanda aka yi wa ƙarin wa’adin aiki bayan sun kai shekara 35 suna aiki, ko kuma sun kai shekara 60 a duniya.

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Kano ta Sanya Ranar Komawa Makarantun Firamare da Sakandire

Ganduje ne ya assasa shirin tsawaita wa’adin aiki a jihar, inda ma’aikata za su iya cigaba da aiki har na tsawon shekara biyar bayan sun kai lokacin ritaya.

Bayan gwamna Abba Yusuf ya ɗare karagar mulki a ranar 29 ga Mayun 2023 ne ya soke wannan ƙudurin, sannan ya yi umarni a dawo da shekarun ritayar shekara 35 ana aiki ko kuma shekara 60 a rayuwa.

Da yake zantawa da manema labarai, Shugaban Ma’aikatan jihar, Abdullahi Musa ya ce bayan an soke ƙudurin ne, aka kafa kwamiti domin kididdige adadin ma’aikatan.

Asibitin Best Choice Ya Kaddamar Da Sabuwar Na’urar Jarirai Ta (Jaundice) Irinta Ta Farko A Arewacin Najeriya

“Bayan bincike ne kwamitinmu ya gano cewa kusan ma’aikata 4,000 suke cikin wannan tsarin, amma za su yi ritaya a 1 ga Disamban 2024. Wannan na nufin a ƙarshen watan Satumba za su miƙa takardar ajiye aiki,” inji shi kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Sai dai Abdullahi Musa ya ƙara da cewa gwamnati ta shirye maye gurbin da za su bari bayan sun yi ritayar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...