Rabon Tallafi a Kano: Kwankwaso ya koka wa shugaba Tinubu

Date:

Daga Kamal Yahaya Zakaria

 

Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya koka da yadda gwamnatin tarayya ta damka rabon kayan tallafi ga yan jam’iyyar APC a jihar Kano.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a jiya lahadi mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata Barau Jibril ya jagoranci rabon kayan tallafi a Jihohin Arewa maso yammacin Nigeria, wanda aka gudanar a Kano.

“Sati guda da ya wuce ina Kano, kuma abin bakin ciki da takaici shi ne yadda Gwamnatin Tarayya ta raba kayan tallafin shinkafa ga Jihohi 35 duk ta baiwa gwamnonin su, amma ban da Jihar Kano.”

2027: PDP ta yiwa Kwankwaso martani mai zafi

“Abun Bakin ciki shi ne yadda tallafin jihar kano aka damka a hannun jiga-jigan jam’iyyar APC su domin su raba. Wannan abun cin fuska ne ga dimokuradiyyar da kuma nuna bangaranci”.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X Wanda kadaura24 ta gani a wannan rana.

Da dumi-dumi: DSS ta kama shugaban kungiyar Kwadagon Nigeria

“Ina kira ga mai girma shugaban kasa da ya gaggauta dakatar da wannan abun domin ya sabawa dimokuradiyya”.

Kwankwaso ya kuma nuna damuwa da yadda a cikin saki uku aka turo daraktocin hukumar DSS Kano 3 kuma ana dauke su, inda ya ce hakan barazana ce babba ga tsaron jihar kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...