Jamiβan hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun kama shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, Joe Ajaero.
PUNCH ta rawaito cewa an kama Ajaero ne a safiyar ranar Litinin a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja, akan hanyar sa ta zuwa kasar Ingila domin gudanar da wani aiki a hukumance.
An bukaci shugaban NLC ya halarci taron kungiyoyin Kwadago da za a yi a Landan, wanda za a fara yau.
Karin bayani na nan tafe