Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Kungiyar Kwadago ta Nigeria ta fitar da wasu matsaya guda hudu da suka cimma a zaman gaggawa da suka gudanar, bayan kama shugaban kungiyar na kasa Kwamaret Joe Ajaero .
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kama shugaban kungiyar Kwadago a filin jirgin sama na Abuja.
Gwamnatin Nigeria dai ta tana zargin shugaban kungiyar kwadagon da hannu wajen shirya zanga-zangar yunwa da aka gudanar a farkon watan Ugustar wannan shekarar.
Yanzu-yanzu: Gwamnatin Kano ta dage ranar komawa da makarantu
A cikin wata sanarwar bayan taro da mataimakin shugaban kungiyar Kwamaret Adeyanjo adewale, ta bayyana Abubuwa hudu da suka cimma.
1. Kungiyar ta ce ta yi Allah wadai da kamun da aka yiwa shugabanta Kwamaret Joe Ajaero , inda ta ce kamun da aka yiwa shugabanta ba ayi shi akan ka’ida ba, saboda ba a bi hanyar da ta dace ba wajen kama shi, kuma bai ma yi laifi ba.
2. Ta bukaci a gaggauta sakin shugaban na ta ba tare da wani sharadi ba nan da karfe 12 na dare na wannan rana ta litinin. Kungiyar ta jaddada cewa Joe Ajaero ba mai laifi ba ne don haka bai chanchanci a kama shi ba. Sannan ta bukaci gwamnatin ta janye karin farashin man fetur da ta yi bakon da ya gabata.
Da dumi-dumi: DSS ta kama shugaban kungiyar Kwadagon Nigeria
3. Kungiyar ta kuma bukaci kungiyoyin farar hula da dauran mambobin kungiyar da su zama cikin shirin tafiya Yajin aiki tare da yin zanga-zangar nuna adawa da abun da gwamnati ta yiwa shugabannasu. Sannan ta ce ba zata lamunci a ci gaba da muzgunawa ya’yanta.
4. Kungiyar za kuma ta gudanar da taron majalisar zartarwarta a gobe talata 10 ga watan Satumba da misalin karfe 09 na safe domin tattaunawa Kan abubunwan da suke faruwa.