Daga Rahama Umar Kwaru
Shugaban kasa Bola Tinubu ya magantu kan karin kudin mai da aka yi a farkon makon nan
Karin kudin man dai yasa ana siyar da lita daya daga Naira 897 a gidajen man NNPC, maimakon 617 da ake siyarwa a baya.
Yayin da a gidajen man ‘yan kasuwa ake siyar da duk Lita kan Naira 1, 200.
Gwamnatin tarayya ta fara sayar da shinkafarta akan Naira 40,000
Da yake bayani yayin ganawa da ‘yan Nijeriya a birnin Beijing na China, Tinubu ya ce karin kudin man “Mataki ne mai tsauri wanda ba a saba gani ba” da ya zama dole don ci gaban Nijeriya.
A sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ambato shi na cewa matakan da gwamnatinsa ke dauka na daga cikin dabarun dora tattalin arzikin Nijeriya bisa turba.
Kotu ta tusa keyar alƙalin bogi zuwa gidan yari a Kano
Sai dai al’ummar Nigeria na ci gaba da kokawa da sabbin manufofin shugaban ƙasar, wadanda suka sanya ƙasar cikin mawuyacin.
Tinubu ya ce nan ba da jimawa yan Nigeriya zasu Fara amfana da sabbin manufofin da aka fito da su don inganta tattalin arzikin kasar.