Yaki da cin hanci: Kungiyar mata Yan jarida ta karrama Muhuyi Magaji

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Kungiyar Mata yan jarida ta kasa ta yabawa shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano Barista Muhyi Magani Rimin Gado bisa nuna karamci da sanin darajar Yan jarida da kuma kokarin da yake na yaki da cin hanci da rashawa.

” Mun gamsu da yadda kake kokari wajen yaki da cin hanci a Kano, Kuma hakan ya nuna kokarinka na ganin jihar Kano ta sami cigaba mai ma’ana hakan tasa muka ga dacewar karramaka da wannan lambar yabo”.

Sakatariyar kungiyar Mata Yan jarida ta kasa Kwamared Wasila Ladan ce ta bayyana hakan lokacin da ta ziyarci Ofishin hukumar.

Yanzu-yanzu:Kotu ta baiwa hukumar zaben Kano umarni Kan zaben kananan hukumomi

Kwamared Wasila ta ce sun ziyarar Muhuyi Magaji Rimin Gado ne domin ne domin ba shi lambar yabo da kuma neman shawarwari da yin jagoranci wurin Isar da sakonsu ga gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf bisa ziyarar da zasu kai gidan gwamnatin Kano tare da Shugabar Mata Yan jarida ta kasa Hajiya Aisha Ibrahim Bura.

” Muna yaba Maka bisa yadda kake mu’amalantar yan jaridu musamman akan aiyukan ka na yaki da cin hanci da rashawa a jihar kano”.

Da yake jawabi shugaban Hukumar karbar korafe-korafe ta jihar Kano Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ya Tabbatar musu zai bi duk wani tsari ba tare da ya shiga aikin kowa ba wurin hadasu da Gwamnan Abba Kabir.

Daga nan ya karfafa musu gwaiwa wajen ganin su Matasa ne, sai dai ya bukace su da jajirce kan aikinsu na jarida saboda muhimmancin da aikin yake da shi. Ya kuma ja Hankalin su wajen gujewa yada labaran karya ko na kanzon kurege don birge wani ko cin mutuncin wasu mutunci.

Gwamnatin Tinubu ta fifita kama masu zanga-zanga maimakon magance matsalar tsaro

Ya Kara da cewa dan jarida ya riki aikinsa da amana domin shi tamkar tsani ne da Al’umma kanji wani sako ko labari ta bakinsu ko hannusu, don haka ya ja hankalin su dasu kasance masu yada labaran gaskiya da inganci.

Karshe yayi godiya da lambar yabo da kungiyar mata yan jarida ta kasa ta Bashi, bisa jagorancin Sakatariyar Mata Yan jarida ta kasa Kwamared Wasila Ladan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika sakon ta’aziyyar Rasuwar Aminu Dantata

Daga Sadiya Ahmad   Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika...

Kungiyar ’Yan Jaridun Kano Arewa ta Aike da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Alhaji Aminu Dantata

  Kungiyar ’Yan Jarida ta Kano Arewa ta bayyana alhinin...

Ku na da rawar takawa wajen inganta Lafiyar al’ummar Kano – Waiya ga jami’an yada labarai

Daga Abubakar Sayeed Kwamishinan Ma'aikatar yada labarai da harkokin cikin...

Ana daf da yin jana’izar Aminu Dantata a Madina

Tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na...