Gwamnatin Tinubu ta fifita kama masu zanga-zanga maimakon magance matsalar tsaro

Date:

 

 

 

Jagoran adawar Najeriya, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin ƙasar da mayar da hankali kan wasu abubuwa da ya kira marasa muhimmanci tare da yin watsi da matsar tsaro da ƙasar ke fama da ita.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon ɗan takarar shugaba ƙasar na jam’iyyar PDP ya yi Allah wadai da harin da mayaƙan Boko Haram suka kai jihar Yobe, da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Ya kuma yi tsokaci kan yawan tashe-tashen hankula da ke ci gaba da faruwa a jihohin Katsina da Sokoto da sauran sassan Arewa.

Atiku ya zargi gwamnati da cewa ta fi damuwa da kama masu zanga-zanga, maimakon magance matsalar rashin tsaro.

“Duk da mummunan zubar da jini da aka yi a Yobe, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, da kuma ɓarnar da aka yi a ƙauyuka da dama a Katsina da Sakoto, da sauran garuruwan da ke yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, da dukkan alamu gwamnati ta fi mayar da hankali kan ayyukanta da sauran abubuwa da ba zu da muhimmanci.” in ji Atiku.

Atiku ya kuma yi nuni da tashe-tashen hankulan da ‘yan Boko Haram ke haifarwa da rigingimun siyasa a kudu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...