Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe wato Grassroot Care and Aid Foundation GCAF tayi Kira ga Gwamnatin Tarayya data gaggauta janye Karin kudin da NNPCL tayi a wannan yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa Wanda asalinsa dama janye Tallafin man fetur da akayi shine sanadin hakan.
Shugaban Gidauniyar Amb. Auwalu Muhd Danlarabawa shi ne ya bayyana hakan yau ga manema labarai domin nuna damuwa da halin da al’umma ke ciki na tsadar rayuwa da hauhawar farashi dama yawan Mutuwa da ake tayi sanadin rashin abinci.
Matatar Dangote za ta samar da lita man fetur miliyan 25 a kowace rana – NMDRA
Amb. Auwalu Muhd Danlarabawa ya Kara da cewa wajibi ne yan majalisu su yi wani abu akan wannan al’amari dare da Gwamnonin da suke Jagorancin al’ummar kasa indai da gaske suke dimokradiyya akeyi.
Idan har baa dauki mataki ba a wannan yanayi to gaskiya alama ta nuna cewar shugabannin da muke dasu ba Imani da tausayin al’ummar kasa a tare dasu.
Sannan ya Kara da Kira ga Yan kwadago da suyi abinda ya dace a wannan gaba na Kira da a janye ko Kuma a tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.