Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Manyan jagororin ‘yan adawa uku a Najeriya na tattaunawa kan yiwuwar yin hadaka wadda zata ba su damar fitar da ‘yan Najeriya daga yunwa da tabarbarewar tsaro gabanin zaben shugaban kasa na 2027, kamar yadda kakakin jam’iyyar PDP ya sanar a ranar Litinin.
Mataimakin kakakin jam’iyyar PDP na kasa Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana hakan a cikin shirin Sunrise Daily na Channels Television a ranar Litinin.
Ya ce ‘yan takarar jam’iyyun adawa uku a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar na PDP, Peter Obi na Labour Party da kuma Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar NNPP, za su ajiye muradun kashin kansu a gefe su kulla kawance mai karfi don tunkarar jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Abdullahi ya ce da a ce shugabannin jam’iyyarsu na baya sun yi abun da ya dace, da tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, Kwankwaso da Obi ba su fice daga jam’iyyar PDP ba kuma da jam’iyyar ta doke Bola Tinubu na jam’iyyar APC a zaben da ya gabata.
Iftila’i: Gobara ta tashin a gidan gwamnatin jihar Katsina
Ya ce, “Mun yi rashin Kwankwaso, mun rasa Peter Obi, duk wadannan mutane, da suna tare da mu a cikin jam’iyyar PDP, da za mu ci zabe.
“APC ta ce sun ci zabe da kuri’u miliyan daya, daya daga cikin wadannan mutanen da na ambata da zai cike mana wannan gibin kuma da yanzu mune akan mulki , kuma da tabbas ‘yan Najeriya ba za su fuskanci wannan matsalar ba”.
Da aka tambaye shi ko PDP na kokarin dawo da Obi, Kwankwaso, Wike da sauran su cikin jam’iyyar, Abdullahi ya ce, “Tabbas ana tattaunawa, za ku ga Peter Obi yana tattaunawa da Atiku, za ku ga Peter Obi yana ganawa da (Nasir) El-Rufai. Gudanar da jam’iyya abu ne mai matukar wahala kuma muna yin iyakacin kokarinmu a cikin kuncin da muka tsinci kanmu. Mun koyi darussanmu ta hanya mai daci.”
A zaben shugaban kasa na 2023, Tinubu, ya zo na daya a jihohi 12 daga cikin 36 na Najeriya, kuma ya samu adadi mai yawa a wasu jihohi da dama da ya samu kuri’u mafi yawa – 8,794,726, kusan kuri’u miliyan biyu fiye da wanda ke bi mashi Atiku Abubakar na jam’iyyar. PDP.
Atiku, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa sau shida, ya samu kuri’u 6,984,520, yayin da Obi, wanda ya tsaya takara karo na farko, ya samu kuri’u 6,101,533 da ba a taba ganin irinsa ba. Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ya zo na hudu, ina ya sami nasara a jiharsa – Kano. Ya samu kuri’u 1,496,687.
Wani abin sha’awa shi ne, Obi da Kwankwaso ‘yan PDP ne watanni kafin zaben da ya gabata amma sun bayyana rashin jituwa a matsayin dalilan da suka sa suka fice daga jam’iyyar.

Waye zai janyewa wani a cikin Atiku Obi, da Kwankwaso ?
Da aka tambaye shi ko me zai faru idan Obi da sauran su suka koma PDP, sai ya ce, “Dole daya daga cikinsu zai ne zai zama dan takarar, sannan daga nan mu samu alkibla.
“Damuwarmu a matsayinmu na shugabannin jam’iyya da kuma wadannan mutanen da na ambata shi ne mu tabbatar da cewa mun ceto ‘yan Najeriya daga wannan kunci da rashin jin dadi da suka addabe su. Ku na ganin rashin iya aiki da rashin sanin yakamata daga bangaren wadannan mutanen da ke tafiyar da kasar nan.”
Bayan shan yabo al’ummar Kano sun shiryawa tsohon Shugaban DSS addu’o’i na musamma
Jigon na PDP ya ce ceto ‘yan Najeriya daga cikin wahalhalun da suke ciki ya fi burin kowane mutum a cikin su ukun.
Ya ce, “Atiku yana cewa idan har ya fi dacewa ya fitar da Nijeriya daga wannan matsalolin to zai yi haka.
“Bai kamata shi (Atiku) ya kasance cikin yan takara ba, Atiku yana cewa hakki ne a gare shi a matsayinsa na mai bin dimokradiyya; kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar masa cewa zai iya tsayawa takara a kowane lokaci.
“Abin da yake kokarin cewa shi ne babu wani abu da zai hana shi takara. Wannan shi ne ainihin hakkinsa na dimokuradiyya amma ba wai yana cewa zai tilasta wa jam’iyya ko kasa ba.
“Ina gaya muku sarai: Peter Obi ya cancanta; idan ya zama dan takara zamu mara masa baya. Atiku ya cancanta kuma idan ya samu tikitin, za mu mara masa baya tare da ba shi goyon bayan da ake bukata domin ceto ‘yan Najeriya daga halin da ake ciki.”