Bayan shan yabo al’ummar Kano sun shiryawa tsohon Shugaban DSS addu’o’i na musamma

Date:

Daga Abubakar Lawan Bichi

 

Al’ummar karamar hukumar Bichi sun gudanar da saukar al’qur’ani mai girma tare da yin addu’o’i na musamman domin yin godiya ga Allah (S W T) bisa yadda ya nufi tsohon shugaban hukumar tsaron farin kaya ta DSS Malam Yusuf Magaji Bichi ya kammala aiki lafiya.

Kadaura24 ta rawaito Limamai, Alarammomi da al’ummar garin Bichi ne suka taru a Babban Masallacin Juma’a dake Bichi domin gudanar Saukar karatun Alqur’ani .ai girma tare da addu’o’i na musamman .

A yayin taron addu’ar Wanda Limamai da Alarammomin sun roki Allah SWA ya kara baiwa Malam Yusuf Magaji wata dama sama da ta baya da kuma ya kammala aikin lafiya.

Masu larurar ido 3,000 ne suka amfana da aikin ido kyauta a kananan hukumomin kura madobi da garin malam

Haka kuma an gabatar da addu’ar ga Mai dakisa Hajiya Aisha Uwar Marayu bisa yadda take taimako marasa gata tare da addu’ar Allah ya kawo zaman lafiya da dorewar tatttalin arziki ga karamar Hukumar Bichi, jihar Kano dama Kasa baki daya.

Taro ya Sami halatar Jama’a da dama cikin harda Shugaban Jami’ar Gwamnatin Tarrayya dake garin Dutsi-ma a Jahar Katsina Ferfesa Arma Ya’u Hamisu Bichi.

 

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar litinin cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya sauke Malam Yusuf Magaji Bichi daga mukamin Babban Darakta na DSS bayan shafe sama da shekaru 5 yana jagorantar hukumar.

Yanzu-yanzu: Hukumar Zaɓe ta sauya lokacin yin zaɓen kananan hukumomin Kano

Shugaban Kasar ya godewa Bichi bisa namijin kokarin da yayi wajen inganta aiyukan hukumar da Kuma samar da walwala ga ma’aikatan hukumar.

Al’ummar jihar kano dai sun jima suna yabawa Yusuf Magaji Bichi bisa yadda ya dauki matasa maza da Mata aikin DSS a jihar, Wanda ake ganin ba a taba samun wani Dan kano da ya samar da aikin yi ga matasa masu tarin yawa a jihar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dan Majalisar tarayya daga Kano ya fice daga jam’iyyar NNPP

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kano Municipal, Injiniya Sagir...

Abin mamaki: Barawo ya sace Motar dake cikin ayarin motocin gidan gwamnatin Kano

Wani barawon mota ya kutsa cikin gidan gwamnatin jihar...

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...