Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin daraktoci na hukumar leken asiri ta kasa (NIA) da na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).
Ambasada Mohammed Mohammed shi ne sabon Darakta-Janar na NIA.
Mista Adeola Oluwatosin Ajayi shi ne sabon Darakta-Janar na DSS.
Shugaba Tinubu ya yi fatan sabbin shugabannin tsaro za su yi aiki tukuru don inganta aiyuka hukumomin, don samar da tsaro ga al’ummar Nigeria.
Shugaban ya mika godiyarsa ga Mayan Daraktocin hukumomin biyu masu barin gado bisa ayyukan da suke yi wa kasa tare da yi musu fatan samun nasara a ayyukansu na gaba.