NAHCON: Samarin Tijjaniyya sun yabawa Tinubu kan mukamin Sheikh Sale Pakistan

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Kungiyar samarin Tijjaniyya ta bayyana nadin da shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu yayiwa Farfesa Abdullahi Sale Pakistan a matsayin shugaban Hukumar aikin hajji na kasa da cewa abune da ya dace.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa daga Kungiyar Samarin Tijjaniyya ta Kasa Mai dauke dasa hannun Sakatare Shehu Tasiu Ishaq da Babban jami’in yada labarai na Kungiyar Abubakar Balarabe Kofar Naisa.

Kungiyar Samarin Tijjaniyya ta Kasa ta bayyana Professor Abdullahi Pakistan da cewar kwararre ne Wanda yasan al’amuran da suka shafi aikin hajji duba da yadda ya rike mukamai daban daban cikinsu harda shugaban Hukumar Kula da Jin dadin al’hazai ta jihar Kano.

Bayan Cire Shugaban NAHCON, Tinubu ya nada wani malamin Addini daga Kano

A don haka ne Kungiyar Samarin Tijjaniyya ta Kasa ta bukaci ya cigaba da nuna gogewar sa domin daga darajar Hukumar aikin hajji ta Kasa tareda kawowa Najeriya cigaba ta wannan fuska.

Sanarwar kazalika ta bukaci sabon Shugaban Hukumar aikin hajji na kasa Professor Pakistan ya zamo babban Jakadan jihar Kano kasancewarsa Dan asalin jihar domin ya zamo abin misali a Kasar nan da duniya Baki daya.

Haka zalika, kungiyar ta ce tadin da Gwamnatin jihar Kano ta yiwa Professor Hafiz Abubakar a Matsayin Mataimakin Chancellor na Jami’ar Yusuf Maitama Sule dake Kano da cewa Abu ne da ake bukatarsa a wannan lokaci.

Kungiyar Samarin Tijjaniyya ta Kasa tace kasancewarsa Wanda ya jagoranci Samar da kafa Jami’ar tun farko, hakan zaisa Professor Abubakar zai kawo tsare tsaren da zasu kawo cigaban Jami’ar.

Yaki da Almubazzaranci da dukiyar al’umma: ICPC ta shirya wa yan jaridun yanar gizo bita a Kano

Haka kuma Kungiyar ta bayyana Professor Hafiz Abubakar da cewa kwararren malamin Jami’a ne da ya rike mukamai daban daban, Wanda yasan harkokin cigaban Jami’a da kuma gudanarwa.

A don haka ne Kungiyar ta bukaci sabon Mataimakin Chancellor na Jami’ar Yusuf Maitama Sule dake Kano ya kawo sauye sauye da zasu kawo daga darajar Jami’ar a duniya kasancewar sa shine dama ya jagoranci kafata tun a shekara ta……

Daganan Kungiyar Samarin Tijjaniyya ta tayi addu’ar samun nasara daga Allah (SWA) da yi masa jagora a wannan sabon matsayi da ya samu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...