Tinubu na Kokarin Mallakawa Kansa Nigeria – Atiku Abubakar

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya zargi shugaban ƙasar, Bola Tinubu da ‘neman mayar da Najeriya mallakin kansa’.

Atiku, ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023 ya yi iƙirarin cewa Tinubu yana jinginar da makoman matasan Najeriya ga kansa da iyalinsa da kuma abokansa na kusa.

Atiku ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe ya fitar a jiya Laraba, inda ya bayyana damuwar sa kan cewa ko bayan Tinubu ya bar mulki, “zai yi wahala a warware abubuwan da ya kafa tare da kuma magance waɗannan matsalolin.”

Atiku ya yi zargin cewa Tinubu na saƙala harkokin kasuwancinsa cikin harkokin gwamnati a Legas, tare da cewar irin hakan ne ke faruwa a yanzu a matakin tarayya.

Atiku ya ce a sanarwar “na yi matuƙar mamaki da gano cewa kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya sanya ayyukansa na sayar da kayayyaki a ƙarƙashin kulawar OVH, wani kamfanin da Oando ke MALLAKIN kashi 49 cikin ɗari.”

“Oando fa yana ƙarkashin jagorancin Wale Tinubu ne, ƙanen Shugaban Tinubu.” in ji sanarwar.

Atiku ya bayyana baƙin cikinsa kan yadda a cewarsa “wasu kamfanoni da ke da kusanci da Tinubu Ssuka dabaibaye harkokin kamfanin NNPCL ba bisa ka’ida ba.”

A wani sakon da ya wallafa a shafin sa na X a ranar Litinin, Atiku ya soki gwamnatin Tinubu kan cire tallafin man fetur wanda shi ne tushen halin da ƴan Najeriya ke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...