Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Amb. Imam Yusuf wanda aka fi sani da Oga Boye ya Ajiye mukaminsa na mai baiwa gwamnan jihar kano shawara kan harkokin matasa.
Ogan Boye ya Mika takardar ajiye aikin nasa ne a Ofishin Sakataren gwamnatin jihar kano a wannan rana ta talata.
Za a shafe kwana uku ana ruwa marka-marka a wasu jihohin Najeriya
Imam Yusuf ya ajiye mukaminsa nasa ne domin ya tsayawa takarar shugabancin Karamar Hukumar Nassarawa a cikin jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya.
Idan za’a iya tunawa dokar Zaɓe ce ta ce dole duk mai sha’awar tsayawa takarar wata kujerar sai ya ajiye duk wani Mukami da aka nada shi kwana 90 kafin zaben.
Badakalar magungunan Kano: Mun fara bincike kuma za mu gurfanar da duk mai hannu – Muhuyi Magaji
Hakan nuni da cewa Ogan Boye ya shiga cikin jerin wadanda suke takarar shugabancin Karamar hukumar Nasarawa a zaɓen da za’a gudanar a ranar 30 ga watan Nuwanba mai zuwa.