Za a shafe kwana uku ana ruwa marka-marka a wasu jihohin Najeriya

Date:

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet), ta yi gargaɗin samun ambaliya a wasu jihohin ƙasar sakamakon mamakon ruwan sama da za a samu kwanan nan.

Hukumar ta ce jihohin da suka haɗa da Kano, da Katsina, da Zamfara, da Jigawa da Kebbi da Kaduna, da kuma jihar Adamawa na cikin barazanar fuskantar ambaliyar ruwa, don haka ne ta yi kira ga mahukuntar jihahin su ɗauki matakan kare al’ummominsu.

Tuni dai dama ambaliyar ta fara ɓarna a wasu jihohin Najeriya inda aka samu asarar rayuka da ta dukiyoyi.

Badakalar magungunan Kano: Mun fara bincike kuma za mu gurfanar da duk mai hannu – Muhuyi Magaji

Alhaji Bashir Idris Garga, darakta a hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriyar NEMA ya ce wannan ruwan saman da za ayi na kwana uku ba ƙaƙautawa zai sanya magudanar ruwa da dama ba a cika damuwa da yashe su ba su cike wanda daga bisani ruwan zai malala har ya je yayi ɓarna.

“Saboda haka ya kamata a ɗauki mataki ƙwarai da gaske ya zama cewa ambaliyar bai yi ɓarna fiye da yadda ake zato ba.” daraktan ya ƙra da cewa.

Bayan Cire Shugaban NAHCON, Tinubu ya nada wani malamin Addini daga Kano

Daraktan ya ce akwai irin wasu matakai da ake ɗauka na gaggawa irin su samun buhani a cika da yashi sai ayi tandagarƙi a canzawa ruwan akala yadda ba zai shiga yayi ɓarna ba.

Darakatan ya ƙara da cewa bayan haka, ya kamata a yashe magudanar ruwa sannan kuma a dage a sanar da ƴan uwa da abokan arziƙi cewa ga sanarwar da aka bayar kuma ya kamata a ɗau matakai.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...