Daga Kamal Yahaya Zakaria
Kamfanin mai na Nigeria NNPC ya ce ya damu matuka bisa yadda ake fuskantar karancin man fetur a wasu sassan Nigeria.
Kamfanin ya bayyana hakan ne a Cikin wata sanarwa da Olufemi Soneye
Babban Jami’in Sadarwa na Kamfanin
Kamfanin mai na NNPC Ltd sanyawa hannu.
Yanzu-yanzu: Tinubu zai tafi kasar Faransa
Ya danganta matsalar da kalubalen aiki rarraba man fetur din.
Kamfanin na NNPCL yana kira ga masu ababen hawa da su kara hakuri, yana aiki ba dare ba rana tare da masu ruwa da tsaki don shawo kan matsalar.
Zargin Sayo Magani: Jam’iyyar APC ta yi wa gwamnatin Kano raddi kan rahoton Dan Bello
Al’ummar wasu sassan Nigeria dai na fuskantar ƙarancin man fetur wanda hakan ya sanya ake sayar da man daga kan Naira 800 har yanzu Naira 950.