Zargin Sayo Magani: Jam’iyyar APC ta yi wa gwamnatin Kano raddi kan rahoton Dan Bello

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Jam’iyyar APC reshen jihar Kano, ta bukaci hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, da ta kaddamar da cikakken bincike kan badakalar baya-bayan nan da ta shafi kashe kudaden da ake zargin na kwangilar samar da magunguna ga kananan hukumomi 44 na jihar.

A wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, shugaban jam’iyyar APC, Alhaji Abdullahi Abbas, ya bukaci a rufe asusun kananan hukumomin jihar domin a daina ci gaba da kwashe dukiyar al’umma da sunan ayyukan hadin gwiwa.

Ya ce amincewar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi na cewa bai san da wannan badakalar ba, wata alama ce da ke nuna cewa ko dai ba shi da iko akan gwamnatin ko kuma rashin iya shugabancin jihar kamar yadda APC take zargi .

Zargin sayo Magani: Gwamnan Kano ya ba da umarnin bincike kan zargin Dan Bello

Abbas ya bayyana cewa umarnin da gwamna ya baiwa hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar kano abun dariya ne.

Shugaban jam’iyyar ya yi nuni da cewa, shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado ya na da bangaranci, kuma ba shi da hurumin bincike kan badakalar da ake zargin yan uwan uban gidan gwamnan kuma jagoran NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Ya yi nuni da cewa wannan badakalar guda kenan cikin jerin zarge-zargen badakaloli da suka dabaibaye jami’an gwamnatin NNPP.

Dalilin da ya sa kotu ta mikawa kamfanin China jiragen Shugaban ƙasar Nigeria

Abdullahi Abbas ya kara da cewa gwamnatin jihar ta bayar da kwangilar aikin gada akan kudi Naira biliyan 27, inda za a gina gada guda biyu a mahadar Dan-Agundi da Tal’udu a cikin babban birni, wanda za a dauko kashi 70 cikin dari na kudaden Kananan hukumomi 44.

Shugaban ya ce har yanzu akwai wasu zarge-zargen kudade da ko dai ba a yi bincike ba ko kuma ba a gudanar da binciken yadda ya kamata ba, wanda kuma suna da alaka da jami’an gwamnatin jihar kano.

Sanarwar ta ce akwai karin zarge-zarge na harkokin kudi da suka hadar da MD Radio Kano da MD ARTV da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...