Daga Sani Idris Maiwaya
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya musanta labarin ba da kwangilar da aka ce an baiwa kananan hukumomin 44 na jihar umarni domin fitar da wasu kudaden don magunguna .
Idan za a yi a jiya asabar wani dan jarida da ke kasar waje mai suna Dr. Bello Habib Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello ya saki wani bidiyo, Inda ya zargi gwamnatin Kano da baiwa kananan hukumomin jihar umarni bayar da kwangilar Naira miliyan 10 ga wani kamfanin mallakin kanin Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso domin samar da magunguna wanda kuna ya ce ba kawo magungunan.
Yadda muka sha matsin lamba kan mu sa INEC ta soke zaɓen shugaban ƙasa na 2023 – Abdussalami
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai Baba Halilu Dantiye da Darakta Janar na yada labarai da yada labarai na gwamna Sanusi Bature Dawakin Tofa suka sanyawa hannu tare, sannan kuma aka aikowa kadaura24 .
Sanarwar tace Gwamnan ya umurci Shugaban Hukumar Korafe-korafen da Yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC) da ya gaggauta bincike kan wannan zargi tare da bayar da rahoton sakamakon binciken don daukar matakin da ya dace.
Gwamna Yusuf ya kuma bukaci al’ummar jihar Kano da su yi hakuri har sai a kammala bincike kan wannan zargi.
A ‘yan wannan kwanakin Dan Bello ya karkato kan yan siyasa inda yake ta yi musu bankada, ko a makon da ya gabata sai da ya zargi tsohuwar gwamnatin jihar kano da almundahanar kudade.